Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sanarwar ta ce umarni ya riga ya fito daga Jagora Mai Girma kuma ba za a iya janye shi ba, jinin shahidai da yaran Gaza da ɗaliban Minab ba zai shude da shudewar lokaci ba, kuma sojojin Amurka a kowane wuri suna cikin halastattun hadafofin kai hari.
Gwagwarmayar Muslunci Ta Iraki (Kata'ib Sayyid al-Shuhada) Ta yi gargaɗin cewa ko dai sojojin Amurka za su bar yankin da ƙasƙanci ko kuma za su koma kasashensu cikin akwatunan gawa, kuma duk wani kuskuren lissafi zai fuskanci matsanancin martani mai halakarwa da ba a taɓa gani ba wanda zai shafi dukkan muradun Amurka a yankin.
Duk sansanoni, radar da cibiyoyin umarni na mamaya a duk faɗin yankin, suna cikin hadafin makamai masu linzami kai tsaye da jiragen marasa matuƙa masu kunar bakin wake na gwagwarmaya; lokaci na kara kurewa babu wata mafaka da za ta cece ku.
............
Ra'ayinka